Kaddara ta chapter 2

KADDARA TA Chapter 2

Yau ma kamar kullum tana sauka a school ta wuce class
dinsu wanda baya rabo da hayaniya da surutai,hankalin ta
kwance ta samu seat ta zauna bata kula kowa ba dan ita
bata fiye shiga shirgin kowa ba a cewar ta itama tata
matsalar ta ishe ta.
Tunda ta dago suka hada ido da Ummi da Mary dake nufu
ta ta hade rai kamar ba ita ce ta shigo yanzu da fuska a
sake ba.
Suna isowa inda take Mary tace da hausar ta bata fita
daidai
"Zufla'u har kin iso?tun dazo muku jiran ki a front door"
Badan taso ba ta danne zuciyar ta ta dago tana kallon su
Mary tace
"Yanzu nima na iso"
Ada dake zaune kan seat din dake kusa dana Zulfa'u tace
"Hope all is well?"
Dan kawar da kai tayi tana fadin
"Yeah"
Tunda ta amsa su ta maida hankalinta kan book din da
take karantawa se dai can qasan zuciyar ta ji take kamar
ta shaqe Ummi dan ita ta gayyato su Mary.
Ana gama lectures din yau taja hannun Ummi zuwa toilet
ran nan nata a bace tunkan su isa Ummi ke fadin
"Zulfa'u ina za muje haka?let off me kar kisa na fadi
mana"
Cike da masifa ta juyu tana fadin
"Ummi don't push me to do wall kisaka nayi abinda bai
kamata ba,ki daina gayyato mun arnayen qawayen ki inda
nake kin san bana son hulda dasu inda karatu ne yaci ace
zuwa yanzu kin haddace,ki daina kawo mun su inda nake
idan ba haka ba duk abinda na muku ke da su ku kuka ja"
Tsaki Ummi tayi tana fadin
"Wai Zulfa'u mesa kike abu kamar wata jahila ne?"
Cike da masifa a fusace tace
"Jahilar ce se me?call me whatever u want amma bazan
gaji da gaya miki ki daina kawo mun su inda nake ba"
Dafe kanta Ummi tayi sannan ta sassauto murya tana
fadin
"Haba Zulfa'u,wani lokaci idan kina wasu abubuwan kamar
ba me hankali ba,Christians dina nan da musulmi duk
Allah ne ya halicce mu kuma bai ce mu qamace su
ba,bayan haka banga abinda suka miki ba amma kin dora
karan tsana akan Christians din nan ba dama su rabe ki
kin dunga wasu irin abubuwa kamar me iskanu haba
Zulfa'u"
Tsaki taja tana fadin
"Ni dai na fada miki indai zaki zo inda nake ki daina
gayyato mun arnayen qawayen ki,tunda baki da wadan da
za kiyi hulda dasu se arna"
Tana kaiwa nan ta wuce fuu kamar iska tayi gida Ummi ta
bita da kallo.
A qufule ta shigo gidan tunda Farida ta kalle ta tasan an
mata wani abun amma ta share kawai dan tasan halin
qanwar tata.
Farida ita ce ta farko a wajen Baban su Alhj.Khalid da
mamar su Haj.Rakiya.
Baban su dan kasuwa ne dake zaune a garin kano wanda
Allah ya bashi rufin asiri daidai gwargado dan bai ragi
iyalinsa da komai ba.
Matan sa biyu Rakiya ita ce ta farko yaranta 4 farida ce ta
farko se Aliu,mariya da kuma Zulfa'u wato last born dinsu
dake zaune wajen yayar tasu a Abuja tana makaranta a
Nile university tana karanta business admin,dan duk wata
dawainiya farida ce ke mata dan ta dawo wajen ta tun
lokacin da tayi aure.
Se matar sa ta biyu wato Karima da yaranta duk maza
Abubakar da Jabir.
Duk yaran gidan mata sunyi aure tun suna gama secondry
amma Zulfa'u ce kawai tayi sa'a baban nasu ya bar ta
qarasa har uni dan yanzu haka ma level 200 zata shiga.
Sa'ar ta daya baban ta yana da mungun sauqin kai banda
mamar su da take me zafi dan abu kadan zaka mata
tahau fada se dai itama wasu lokutan akwai sauqin kai.
Tana da wata dabi'a na rashin son wanda ba musulmi ba
dan ko yaya ka rabe ta se ta nuna maka,se dai tana da
sauqin kai wasu lokutan amma abu kadan ne ke sata fushi
a wani lokacin.
Haka ma yayan ta Aliu dan shima kusan halin su daya
basa son hulda da wanda ba musulmi ba har abun nasu
ya so yayi yawa.

No comments:

Post a Comment