🏵MEKE FARUWA 05🏵 Kamar wasa ya kuma tada daki ashe zai cika ne wannan karon 'yar yarinya ya dauko musu daga kauyan Turunku Mara kunya nan suka hada kai su uku suna mata habaici wai juya su kam sai zazzaga haihuwa suke, cikin ikon Allah sai ga Fatima itama ta wayi gari da ciki. Kwanci tashi har haihuwa tazo, komai na gama da ciki don kayan yara duk ita ta siya, domin da ta tambaye shi cewa yayi shi dama bai taba sayan kayan jarirai ba kuma kanta ba zai fara ba. Suko sauran kishiyoyin nata sai zundenta suke wai ba saban ba su wance anyi ciki. Bisa ga yardar Ubangiji ta haifi'yarta ita daya kuma cikin dare, maigidan dama dakin Amarya yake, ita ce ta yanke cibi da kanta dama tana da sabuwar rezarta, sannan in ta zaga sasan Goggo sasa takan tambaye ta yanda zata yanke cibi saboda ko zata haihu cikin dare, ba zata samu mai kira mata Goggo ba. Ta nade' yarta cikin zani da ta huta ta tashi ta kwashe jinin. Da Asubahi Allah ya kara mata karfin jiki ta fito ta dora ruwan wanka, ta wanke 'yarta mai matukar kyau sunusi babban yaron maigidan nasa dan gidan Ladiyo ya leko wai in ji Goggo salame ( amaryarsu kenan) ta ce ki bata kwanon koko, ta ce babanka fa? Ya ce ta yana dakinta ta ce kaje ga kwanonin ka kai sannan ka ce babanku yazo na haihu, da murna yaron ya tafi kun San yara da dokin haihuwa, sai ko gashi ya shigo ba yabo babu fallasa fuskarshi ya dauki yarinyar ya gani ba ko addu'a ya aje ta kilama bai iya addu'ar ba ta ce don Allah ka siyo min dan kayanta mana? Ya dube ta ke Fatima dube ni ba kanki na soma haihuwa ba, bare ki min tsurfa in za ki sha kunu kisha duk sauran kunu ake dama musu. Ta ce to yanzu wa zai je ya fado ma'yan Bauchi? Ya ce wannan kuma ya rage naki, ni dai bani da kudi haihuwar nan ma ki samu ko masarar fate in Samar miki kada ki sa rai zan yi wata karya dan bani da hali. Ta dube shi cikin takaici tare da da na sanin auranshi. Ta ce duk matan ka ka fifita su kai na, domin ganin idona kana sai musu kayan (shayi) sannan ka musu ragon suna har ma da dan dinkin suna, ban sani ba ko sun fini yi maka biyayya ne? Tsaki yayi sannan yayi waje, tayi ta tashi wani dan saurayi jikan Goggon sasa ta mishi kwatance ya tafi Bauchi don shaida ma iyayanta. Washe gari kanwar Umma ta biyo dan aike suka dawo ta ci gaba da kula da ita a zaman Inna hausi ta tabbatar Fatima tana matukar hakuri domin komai da kanta take saye don abincin gidan nasu baya ciyo ga Inna hausi sai daiu su yi yar miyarsu haka ake har suna tun ana gobe yan Bauchi suka zo, masara kurum ya miko ko gishiri bai bada ba ita ce ta yi komai, dangi sun hada mata shatara ta arziki, ya kuwa ta ce suna Bilkisu mai gadon zinari. Tubarkalla Masha Allah haka kowa ya ke cewa in ya ga Bilkisu shi ko ubanta ko kaza bai yanka mata ba bare rago amma ta zuba ido kuma ta bar ma Allah. Haka Bilkisu ta taso cikin sha'awa da kuma birgewa amma gurin uwarta domin mahaifinta bai taba mata ko da wasa ba daga nesa bare ya dauke ta, a haka ta kuma samun cikin Sakina sannan Maryam sunnan Umma ne don haka suke kiran ta momy, sai Ku Asma'u lokacin tana goyon Asma'u abubuwa sun mata yawa ga yara maigidan baya biya musu bukatun 'ya'yansu cima ba dadi, in kana son ci da dan galmi sai ka bude bakin jakarka yara babu karatu su sun usima da suke maiya ya dai saka su amma ya bar iyayan da siyan takarda da biyan dan kudin jarabawa, don haka suka hana yaran zuwa makaranta kowacce ta kama Sana'a tana dora ma ya'yanta suke nan da yake son su bare Fatima wadda ita da ban za duk daya, gidan Hajara ta shiga wato aminiyarta, suka shawarta tace hajara shawara na kawo miki, ta ce ina jin ki Fatima, tace kina dai kallon rayuwar da muke yi a gidanmu. Ba cin kirki sai gasar haihuwa, to ba zan iya ba so nake don Allah ki ma Malam maigidan ki magana ya taimaka min da wani dan taimako haihuwar nan ta tsaya in samu in ji da tarbiyar wadannan ma balle ni mai'ya'ya mata ta ce kin yi tunani zan ko gaya mishi haka ko aka yi rubutu yayi mata haihuwar ta tsaya ta samu ta saka Bilkisu firamare.. 🏵MEKE FARUWA 06 🏵 Sana'o'i ta ringa yi sbulu, omo, manja,mangyada, lallai ana shan wahala da rayuwa,haka nan tayi ta kula da yaranta har suka soma tasawa. wata karamar sallah tazo nan ta shirya ita da yaranta, don zuwa bauchi, Bilkisu yarinya mai kyau da shiga zuci, lokacin shekarunta biyar, kawunta Aminu ya tafi da ita kallon hawan sallah, tana sha'awar kallon hawa ko a zariya tana son zuwa amma Mamanmu bata bari haka suke ce ma fatima, ba wanda ya burge Bilkisu gurin kallon hawan nan kamar wani dan yaron sarki ba zai fi shekara biyar ba tsaran ta kenan, an mishi nadi shima cikin wata alkyabba bayan shi runduna ce guda, yaron yana ta daga ma mutane hannu, itama sai daga hannu take tana mishi bye-bye, ai ko kullum bata da labari sai na Yarima. haka kawunta ya ce mata sunanshi har suka bar bauchi suka dawo zariya lbrin yarima take yi haka nan kuma sai ta shiga yin mafarkin yarima. kullum ta kwanta sai tace tayi mafarki sun wasa da yarima har abin ya ishi mamanmu tace kada in kuma jin zance yariman nan, don haka ko tayi sai tayi shiru. kowane sassa zundenta suke wai ta ki dora ma yara talla gata da ya'ya mata, in ta tashi aurar da su saga ni me zata kai ma ya'ya daki? sam wannan bai damu mamanmu ba ita dai burinta shine taga 'ya'yanta sun samu tarbiya tare da kulawa. Bilkisu yarinya ce mai tsananin hakuri da zurfin ciki, tana da kwazon karatu da son karatu, sabanin Sakina mai fada da kin raini don haka duk kishiyoyin mamanmu ta tsane su matuka, Maryam ko sai dai fushi da miskilanci. Asma'u auta itama akwai tsiwa tun tana karamarta, yanda yayyinu suk dukan Bilkisu sai dai ta yi kuka. Asma'u kam bata raga ma abokan goyonta shi yasa rigima kullum. Salame ta shiga dakin karima tana fadin ke 'yar gari king uwar mata? Me tayi? In ji karima bayan ta bada dukkan hnkalinta, Yau kuma takalma silifas sababbi ta sai musu. kan ta yi magana sai ga Ladiyo, kunga uwar mata? A gindinsu zata kare an siyo musu silifa. Karima taja tsaki ai ta haifar ma kanta wahala mata kai ta musu bauta ko gidan Miji suka je ba ka huta ba, mu ko masu mazan da farko in sun kawo karfi sai dai mu kwanta su mana su ma kannansu matan. salame ta ce ai Allah ya taimake mu da muka fara da maza. Ladiyo ta ce ni duk ba wannan ya dame ni ba, irin in ma kalli Bilkisun nan yarinya kyau tamkar aljana? salame ta ce kuma tafi sonta ba, tsorona daya kada wani mai halin ya aure t. Ladiyo tace kada nima ina wannan tunanin amma ga shawara ta rada musu wata magana a kunnuwansu, suka saki dariya tare da fadin kin kawo shawara. Bilkisu da kannanta cikin kayan islamiya suka nufi islamiyya, sai da ta raka kannanta kofar ajinsu Sakina da mami, sannan ta tafi ajinsu, duk malaman makarantar sun son Bilkisu saboda kokarinta tare da hazaka ga ladabi ga kuma tsafta duk da cewa kayan makarantar tasu sun tsufa amma tsaf suke a wanke. ta shiga suka soma karatu, basu dade ba wani malami ya shiga da wata yarinya sabuwar zuwa ce, duk ba zata fi Bilkisu ba, ta shigo tana yan kalle-kalle alamun bakunta Bilkisu ta kalle ta cike da murmushi,
🏵MEKE FARUWA 07 🏵
don haka sai ta je ta zauna kusa da bilkisu. Bayan sun tashi sun fita bilkisu tace yaya sununki? Ta ce Mansura Sadik, ke fa? Ta ce ni sunana B M S, da fatan zamu zama kawaye? Mansura cikin murna ta ce. Insha Allahu. Ta debo kannanta itama da kaninta Abba ta dakko shi daga ajin da aka kaishi suka jero suna hira. Gidan su Mansura ba shi da nisa da islamiya, don haka Mansura ta roki Bilkisu ta shigo ta gaida Ummanta, jikin Bilkisu yayi sanyi da ganin daular da su Mansura suke ciki, lallai Mansura ba abokiyar yinta bace, domin an ce kwarya ta bi kwary. hajiya mero mahaifyar mansura nurse ce mahaifinta kuwa ma'aikaci ne a {G T Bank} da ke kaduna.
makarantar bokonsu ta kudi ce mai tsada, haka ne yasa Bilkisu dan Jan jiki da Mansura, amma Mansura sai ta kara shige ma Bilkisu ta ki sai wata rana bata da lafiya don haka bata samu zuwa islamiyya ba hankalin Mansura ya tashi don haka kuwa ana tashi ta bi su Sakina don ta dubo Bilkisu. Sam Mansura bata damu da yanda taga gidan su Bilkisu ba, har ma da ta samu Mamanmu ta gama tuwo sai da taci, hakan ya sanyaya zuciyar Bilkisu don tana son Mansura musamman ma da ya ke Mansura iyayanta sun kasance yan gombe, tana ganin gombe da Bauchi kamar daya ne gunta tana son yan Bauchi dangin uwa masu sonta, tana ganin kamar bata da masu sonta sai yan Bauchi shi yasa duk inda ta ga yan Bauchi tana girmamamasu, Mansura tana da son tuwo don haka sai ta samu gurin zuwa.
Ko Bilkisu bata nan Mansura tana zuwa gurin Mamanmu jin ta take tamkar mahifiyarta waton Ummanta suka niyan gidan sai suka tsiri sakin habaici, Bilkisu ma nan ta saki jiki da Umma Umma da Mamanmu suka zama kawaye, haka ya sosa ran su Ladiyo musamman da suka ga tana basu kayan sawa zuwa dan abin marmari.
Bilkisu tana zaune ciki wani ciyayi mai kama da cafet guri sanyi da iska yanda yake Kore fatau ya bata sha'awa ga fararan tattabaru suna tashi wasu suna sauka. Can daga nesa sosai take hango dan matashin yaron tasaranta bisa kan doki yana isowa gurinta ya tsaya cike jin kai. Yace ke wa ya kawo ki gonata?
Ta dube shi nan ne gonarka? Kafin ya bata amsa sai ga wasu mutane su biyu suka kama mishi linzamin doki ya sauka, sannan ya isa wata kujera dake can gefe irin ta sarakannan ya zauna sai ga wasu mutane cikin jaja yan kaya sun tsaya a bayanshi, can kuma sai yace na sallame Ku. Suna tafiya ya dawo gurin Bilkisu ya zauna kusa da ita ke yar sakin wane lardi ne? Ta dube shi ba ni da alaka da sarauta. Ta bashi amsa, yace kin sanni? Ta dube shi cike da mamaki kai ba ka da gane mutane so nawa muna wasa da kai? Firgigita ta farka daga bacci yau mafarkinta ba irin na sauran ranaku ba ne, domin sauran ranakun tafi mafarkin suna wasan kwallon kafa, ko na raga koma na tebur, suna hira sosai, amma ya kan nuna bai ma Santa ba ne, tayi murmushi, tun tana yar shekara shidda take mafarkin Yarima gashi yanzun tana shekarar karshe a primary shekarar haihuwa kuwa sha daya su Bilkisu an soma zama yammata, kyanta kullum karuwa yake yi.
Hankalin mamanmu ya tashi domin ba ta da kudin da zata yi ma Bilkisu hidima dan zuwa secondary, duk da cewa ta ci domin makarantun gwamantin ma wannan zamanin sai kana da hali. Da kanta taje makarantar da Bilkisun ta ci sun mata lissafin tun daga rijista zuwa uniform da takardu dubu takwas har da dori. Hankalinta ya tashi bata da inda zata samo kudin nan, gidan hajara kawarta ta shiga don yin shawara, hajara ta bata shawarar me zai hana Bilkisu ta yi aikin gida ko na wata uku ne, in yaso sai ta shiga a zango na biyu tun da an amso form. Mamanmu jarumar uwa ce wacce samun kamarta sai an tona, tsamaranta cewa zata zamar wa ya'yanta uwa kuma uba, don haka ta ce ma hajara ni zan yi aikin da kaina wa ki ke ganin zan samu ya nemo min aiki? Hajara ta ce kada ki damu akwai mata masu hali da suke zuwa gurin malam zan dinga musu magana har a dace, shin maigidan naku zai barki?
🏵MEKE FARUWA 08 🏵 Ta ce tunda ba bani zai yi ba ai batun hanawa ma bata taso ba, shi fa yanda na kula koma menene kije kiyi amma kada ki tambaye shi, sukansu kishiyoyin nawa da yake sonsu baya musu komai, amma don rashin tunani suna nan suna ta zabga gasar haihuwa,yaran bacin kirki bare sutura, karatu kuwa sai dai na zagi ashar kam, kwando-kwando za ki ga dan karamin yaro yana saukewa, gaskiya 'yan gidanmu su ne suke bata ma zage zagi suna, shin haka kowane gida suke yi? Hajara tace a'a akwai dai masu yin amma ba duka ba.. Cike da farin ciki tabar gidan hajara, ta samu Bilkisu da yan kannanta a cikin daki, tana koya musu darasin lissafi, nan ta zayyane ma Bilkisu komai, Bilki ta ce mamanmu ki bari ni nayi aikin in an samu, ta ce a'a nafi soe ni in yi bana son kije ki bata ma masu gidan har su sallame ki, bukatarmu ya zama bata biya ba. tace mamanmu amma kinsan bana fada ko? tace na sani maigado, amma ki bari sai dai an samu din kisan ke yarinya ce ba kowane abu ne zaki iya yin shi ba. Sallamar Mansura ta katse su, suka amsa ta shigo kusa da mamanmu ta zauna sannan tce mamanmu ina kwana? Suja gaisa ta dubi Bilkisu tace "Bily ya dai, yaushe zaki fara shiga school ni dai on monday zan fara zuwa. Bilki tace ni kam ba rana Mansu, kila ma sai second term. Mansura tace akan me? Tace kudi, mamanmu tace kin san ko mai yanzu sai da kudi ana cewa ne dai makarantar gwamnati amma suma duk shegiyar darin ce ga kudin motan zuwa makaranta kullum mansura tace bari Abbanmu yazo week end zan gaya masa. Bilki har suna hada baki da mamanmu, a'a kar ki yi masa magana shima yana ji da nasa iyalin. Mansura tayi shiru, amma a ranta ta raya sai ta fada mashi... Haka kuwa yana dawowa ta gaya mishi, ya tambaye ta ko njawa suke nema? Ta ce ya basu kowanne ita dai bata sani ba, kuma ta san ko ta tambaye su ba zasu fada ba. Dubu goma ya bata yace, gashi ki basu." sai da ta kai kudin mamanmu da yaranta suka je suyi godiya,Bilki kuwa sai da tayi kukan murna, sannan tana ta mamakin dama da gaske ne akwai iyaye masu yiwa 'ya'yansu hidima? Ba sabanin iyayansu mata da wahala? Cikin nasara ta shiga j.s.1 mansura kullum in za su je makaranta sai ta saka direbansu ya biyo sun dauki Bily, sunan da ta ke kiran bilkisu kenan, ita kuma Bilki tace Mansu, wani abin da yake kara ba Bilkisu mamaki shi ne, yanda mafarkin Yarima ke kara yawaita a gare ta, ko gyangyadi take sai ta yi bare barcin dare. saboda sabon da suka yi har ta saka mishi Yarima aboki, shi ko yana kiranta Beauty, tana son sanar da mamanmu amma tasan mamanmu zata ce shirme ne, shi yasa take bar ma cikinta don ko mansu bata taba ba wa lbri ba. cikin haka hajara tazo ta ce, an samu aiki. Mamanmu tace ai ko zan yi, 🏵MEKE FARUWA 09 🏵 Suka je gidan hajara inda hajiyar da za a yiwa aikin take jiransu.Bayan sun gaisa tadubi mamanmu tayaba da tsaftarta don haka tace girki nake so zaki iya? Mamanmu tace me zai hana.Nan suka sasanta ita da hajiya kilishi, gidanta na nan tudun wada, sun sasanta kan dubu uku, kuma za'a dinga zuwa ana daukarta haka nan za'a dawo da ita ko da ta samu maigidan nasu da batun sai yace,shi ina ruwan shi,ta dai sani dole ran girkinta tazo shima ta mishi,dama tasan haka zai ce,tunda shi dama baya son ma mace tace ko da bani kudin kamu,wani lokaci takan zauna tana tunani, anya maigidansu yana son lahirarshi ta mishi kyau?In'yan abinshi suja motsa haka zai je ya nado tsiranshi yazo ya zauna gaban'ya'yanshi yana ci ba zai sammusu ba in ma yaga suna kallonshi sai yace kai daina kallona ka da ka saka ni in kware.Ko ya fita bakin titi da yamma ya sayi doyarshi da kwai ya zauna yana ci in an ce yara suzo suce yaba da kudin cefane sai yace kai zauna nan kayi wasan ka shareta,kuma fa in yaron nan ya zauna haka zai cinye ya hana yaron, halin wannan mutum sai shi hakika baici sunnanshi ba. Cikin sa'a Mamanmu ta soma aiki tana tafiya da safe in yaranta sun tafi makaranta da sha biyu suke maidota gida, in ta gama musu abincin rana domin tana son ta zo ta sallam yaranta. hajiya kilishi kan ce Dibar musu ki kai musu. Sannan karfe hudu zata koma tayi na dare, in ranar girkinta ne kuma sai shida take tafiya don ta samu ta gama na gida. Su kam su ladiyo, nan suka soma nuna hassada tare da canza mata suna daga uwar mata zuwa boyi. Su yi ta mata habaici tare da maganganu marasa dadi, kafin wani lokaci mamanmu da 'ya'yanta sun canza,sunyi kyau, saboda cima ta canza in ta kawo abincin takan dibar musu ta mika ma ladiyo tace su ba wa yara, suna zaginta suna komai haka zaki ga suna kason su sai kace daukin nama su da ya'yan suna ci tandar harshe. Hajiya kilishi tana da yara mata kusan sa'annin su Bilkisu don haka suna samun kaya. Rayuwa dai ta canza yanzu har da sabulu mai kamshi suke wanka. Cikin haka suka shiga J.S 2 lokacin alamun girma ya soma shigar ma Bilkisu, kyanta ya soma bayyana, duk layin kowa sai zancenta yake yi, sun kuma kara shakuwa da mansura duk in da kaga zara za ka ga wata.Bilkisu tana da kulafucin karatu don haka bata da lokacin komai sai na karatu. Azumi ya matso gashi, lokacin ana fama da rashin kudi a gari, 'yar doyar da maigidan ya kawo buhu daya ce, nan ya kasata gida hudu yace kowa ya kwasa sannan kada wacce tai mishi zancan geron kunu domin ba shi dashi, cikin haka Azumi ya kama. Saboda rashin hankalin su ladiyo sai suka ce ma maigidan su fa kowa tayi girkinta kenan suna kyashin taimakon juna, maigida yace wannan lalurarsu. Mamanmu ta ji dadin hakan domin ya'yanta hudu ne,kuma dama aiki yana mata yawa,ranar girkinta yanzu kam hajiya kilishi tace ki dinga hada girkin tare da yaranki,dama ga alale da kunun tsamiya na sadaka da ake yi ana bai wa al'ummar Annabi sai kurum ta huta da yin girki biyu,in ma dakinta yake sai ta dibi nashi cikin kwano samira da kunu a kofi. Bilkisu taje ta amso, wataran ta roki direban ya kawo nan zaka ga malam maman an baza tabarma tsakar gida ana kwasar gara, cefanan wani kai ka kasa, haka matan ke ce mishi,in sunga yana rawar kan cin abinci ran girkin mamanmu,haka nan mijinta da yayi rabon kayan azumi shinkafa, masara,gero,da kuma suga sai daya ba mamanmu kowanne buhu,jikin kishiyoyinta ya dauki bari bakin cikinsu ya kasa boyuwa ita kam kowa sai da ta dibar mishi har 'yan sauran sassan da su rukarta su goggon sasa tare da matan yayyin maigidan nasu da na kannai. Wato mamanmu mace ce mai rama alkairi ga duk wanda ya mata sharri, tana da matukar hakuri tare da sanin ya kamata, in ban da haka yanda kishiyoyin nan nata suke mata kai har shi kanshi maigidan yafi mata wulakanci akan sauran kishiyoyin nata, amma hakan bai sa tayi tunanin cin zarafinshi ko kishiyoyin ta ba sai ma kyautata musun da take yi, shi yasa kullum cikin ci gaba take. Hatta abincin sadaka ko nata in tayi sai ta basu..
