Kaddara ta chapter 4

KADDARA TA Chapter 4

Yau ma da bakin ciki ta tashi dan sam barcin bai ishe ta
ba,hakan nan ta shirya ta samu su Anti farida suna
karyawa,sama2 suka yi tadi driver ya wuce dasu school.
Amma data dawo da murnar ta dan yau sun gama exams
se kuma jiran result.
____
10:00 Zulfa'u ta yi wanka cikin wasu riga da skirt kalar
maroon,irin shigar nan tata data saba se ta daura black
vail ta sauko qasa.
A parlour ta tarrar da Anti farida dake fama dasu fudel
kasancewar weekend ne.
Zama tayi a kujera tana fadin
"Fudel zo"
Da gudu kowa yazo ya hau kan cinyar ta yana dariya tana
shafa kansa tace
"Abar mommy ta huta koh?"
Daga mata kai yayi yana wasa da button din rigar ta yana
fadin
"Mum let's go shopping today"
Hada ido da Anti farida suka yi nan da nan suka sa dariya
Zulfa'u tana jan hancin sa tace
"Ba yau ba,mu jira daddy ya dawo gobe se muje shopping
koh?"
Nan suka hau murna suna tsalle dan baban su bai fiye
zama a gida ba yawanci yana tafiye2 dan costume ne
Allah ya bashi arziki.
"Yawwa Zulfa'u tashi kije wajen maman habiba ki kai mata
wannan kice gashi na manta ban kawo mata ba tun jiya
se yau na samu"
Wani dan bowl ta miqo mata
"Anti farida wannan din menene?"
"Kanwa ce mana,ki tashi ki kai mata kina wasting time tun
jiya fa ta tambaye ni da safe"
Tashi tayi hade da daukar bowl din tayi site din.
Tana zuwa bakin qofar ta danna door bell wajen sau uku
tana dannawa daga ciki taji ana fadin
"Come in"
Shiru tayi na wasu seconds dan idan bata manta ba irin
muryar nan taji jiya amma se kawai ta murda handle din
hade da yin sallama.
Tsayawa tayi tana bin parlourn da kallo dan komai an
canja se dai iri daya ne da nasu se din canja canja da ba'a
rasa ba.
Kudi da suna magana da tuni nan gidan ya fara dan ya
tsaro iya tsarowa ba shirgi se komai da yake a mazaunin
sa.
A cikin seconds din da basu gaza 6 ba ta qarewa parlourn
kallo sannan ta maida kallon ta ga kujerar da mutumin
dake zaune wanda hannun sa riqe da Mug da alama
coffee yake sha.
Riga ce T-shirt a jikin sa se wando iya gwaiwa,ya hakimce
a kan kujerar idon sa kan tv.
Kasa dauke idon ta tayi a kansa dan fari ne wanda ya
matukar dacewa dashi.
Iya kyau ya hadu dan kyakkyawa ne nesa ba kusa ba
kuma shigar da yayi seya qara fiddo da ainihin surrar jikin
sa da take a murde kamar body builder,duk da bawai kato
bane amma baza a ce masa siriri ba kansa ya tara suma
da kuma saje daya zagaye kyakkyawar fuskar tasa wuyan
sa sanye da chain kana gani kuma kasan gold ce.
Bai amsa mata sallamar ba hasalima miqewa tsaye yayi
yana shan coffee dinsa hankali kwance kamar bai san da
ita a wajen ba.
Nan da nan ran Zulfa'u ya baci gannin yadda ya maida ita
tamkar wata gunki a wajen.
"Wa'alai kumussalam"
Salamar da aka ansa ne daga saman stair case din yasa
Zulfa'u maida kallon ta wajen.
Wata mata ce ta fito sanye da atampa blue wacca ta
matukar yi mata kyau dan fara ce sosai kana gannin ta
kasan sun hada jini da wanda ke zaune a kujerar.
Dan murmushi Zulfa'u tayi bayan matar ta iso inda take
wanda itama murmushin bai bar fuskar ta ba.
"Emmata"
Daga jin yadda ta fadi emmatan kasan hausar bata zauna
sosai a bakin ta ba,dan murmushi Zulfa'u tayi tana fadin
"Good morning ma"
"Morning how're u?"
"I'm fine"
Sannan ta miqa mata bowl din tana fadin
"Gashi tace na kawo miki tace kiyi hakuri mantawa tayi"
Karba tayi tana fadin
"Oh Allah sarki kice mata na gode"
Murmushi tayi sannan ta dan kalli shi yana nan tsaye a
wajen,se a sannan taga tsayi ne dashi bana wasa ba dan
dogu ne sosai masa Allah se ya qara masa kyau nesa ba
kusa ba.
"What's ur name?"
"Zulfa'u"
Dan murmushi tayi tana fadin
"You have a nice name and u look alike u resemble each
other,is she ur sister?"
Dan murmushi tayi tana daga mata kai alamun eh sannan
tace
"Thank u ma"
Dafa kafadar ta tayi sannan tace
"Jira bari na kawo miki bowl din"
Juyuwa tayi tana kallon saurayin dake tsaye yana kallon tv
tace
"Honey take this to the kitchen"
Juyuwa yayi yana kallon ta ba tare da ya kalli Zulfa'u dake
tsaye a gefen ta ba yace
"Ok mum i'm coming"
Dan bata fuska tayi tana fadin
"Baka iya yiwa baki magana ba,can't u say hi to our
neighbour,Zulfa'u"
Kallon sa ya kai kan Zulfa'u dake tsaye a wajen har a
lokacin tana binsa da kallo yace
"Hi"
Sannan tace
"Meet my son Christoph"
Kallon sa take sannan tace masa itama
"Hi"
Bata fuska tayi tana fadin
"Haka ake gaishe da baki a garin ku koh?"
Dafe kansa yayi yana fadin
"Oh Gosh Anti Mary,what did u wan me to say again?"
Kawai ya karbe bowl din yayi kitchen dashi Zulfa'u ta raka
shi da ido hade da tabe baki.
Murmushi tayi tana kallon Zulfa'u hade da rage murya
tana fadin
"Yaran zamani"
Itama dan murmushi tayi,yana fitowa daga kitchen din ya
miqa mata sannan yayi stair case din dan gudu2 har
ginnin yana dom dom yaji takon maza.
"Ya school?"
Ta fada tana kallon Zulfa'u
"Alhamdulillah muna hutu"
Kallon ta sosai take sannan tace
"Ohkay kuna hutu shiyasa bana gannin ki sosai amma zaki
na shigowa koh?"
Daga mata kai tayi tana fadin
"Eh zan na shigowa"
"Yawwa baby girl kice mata na gode sosai koh?"
Daga mata kai kawai tayi sannan tayi ficewar ta,amma
tana mamakin dan ta ne wannan gardin.
Shigowa parlourn tayi da sallama se data zauna sannan
tace
"Tace ta gode"
Murmushi Anti farida tayi tana fadin
"Kinga maman habiba yau tana da kirki koh?"
Dan murmushi tayi tana jinjina kanta alamar eh,amma
har yanzu tunanin su bai bar brain dinta ba.

No comments:

Post a Comment