KADDARA TA Chapter 5
Tana zaune a parlour waya ce a hannun ta tana
dannawa,saukowa da Anti farida tayi cikin shiri hannun ta
riqe dana su Fudel da Fausam kamar wasu twins dan
Fausam ne first born se Fudel tazarar 1 year ne a tsakanin
su shiyasa idan ka gansu zaka ce kansu daya shekarar
Fausam 5 Fudel kuma 4.
Kallon su take tana murmushi ta ajiye wayar ta a gefe
sannan ta daga Fudel sama suna dariya sannan ta ajiye
shi tana fadin
"Anti farida se tafiya kenan?"
Gyara mayafin ta take tace
"Tafiya za muyi se ki mana gadin gidan"
Dariya suka yi har mota ta raka su dan ita ce zata yi
driving.
Zulfa'u ta dan bata fuska tana fadin
"Anti ni kadai zan zauna?"
Hararar ta tayi tana fadin
"Me zai cinye ki a gidan?"
Dariya tayi sannan tace
"Salim ma zan kira kwana biyu bai zo ba"
Riqe baki Anti farida tayi tana fadin
"Lallai kam,ki ce masa munyi hannun riga tunda kwana
biyu ya manta da mu"
Dariya kawai tayi hade da daga musu hannu har motar ta
fice sannan ta koma ciki ta kira Salim.
30 mins ya kira ta yace yazo.
Daukar vail dinta tayi dan wasu riga ce iya gwiwar ta me
dugun hannu kalar black and white se kuma straight skirt
ko kwalliya bata yi ba ta dan fesa turare sannan ta fito.
Motar sa qirarrar corolla kalar fara ce yayi parking,tunda
ta fito ta hango wadanan zaune can zaune kan kujera se
table da wasu abubuwa akai ko ba'a fada mata ba tasan
taba suke sha.
Su 5 se dariya suke suna tadi da alama yanayin yana
musu dadi,kallo daya ta musu ta dauke kai hade da jan
tsaki.
Gannin ta fito yasa Salim fitowa daga motar ya jingina
jikin motar yayi folding arms dinsa yana binta da kallo.
Salim yana da kyau dan fari ne se dai ba sosai ba yana da
tsayi kuma ba kato bane dan siriri ne yana da son tara
suma se dai ba sosai ba,yayi kyau cikin qanan kayan da
ya saka sun amshe shi matuqa.
Saukar da kanta qasa tayi bayan ta iso inda yake gannin
irin kallon da yake mata.
"Ka shigo ciki mana"
Ta fada tana kallon sa
"A'ah ba se na shiga ba bana so mu hadu da Anti farida
na mata laifi"
Dan murmushi tayi tana gyara zaman eyeglasses dinta
sannan tace
"Ai kowa tana nan tana jiran ka da irin punishment din da
zata baka"
Dariya suka yi wanda a lokacin Zulfa'u ta dago cikin eye
glasses dinta suka hada ido da daya daga cikin su
Christoph,dan ko ba'a fada mata ba tasan maganar su
suke gannin irin kallon da suke musu,dauke kai tayi suka
cigaba da magana da Salim.
"Guy who're does?your neighbours huh?"
Inji Daniel daya dauke cup yana shan ruwa hade da kallon
Christoph dake danna waya wanda hankalin sa ma baya
inda suke.Se a lokacin ya dago ya kalle su Zulfa'u dake
hirar su hankali kwance,lokaci daya ya dauke kai hade da
fadin
"Maybe"
Favour dake shan cigarette ya dan yi dariya yana fadin
"Wannan small pikin hira ta fito"
Tabe baki Christoph yayi yana fadin
"Child abuse"
Dariya suka sa banda Christoph daya hade rai Wale dake
buga whot shida Mercy yace
"Ina ruwanka dasu hadda wani wannan child abuse ne?are
u jelouse?"
Wani kallo yayi masa wanda yasa suka qara shekewa da
wata dariyar,ya wani bata fuska yana fadin
"This girl is not my type she's a muzlim and u know i don't
like fat girls,besides i don't like girls who where glasses"
Mercy ya dan kalli Zulfa'u na tsawan wasu seconds din
kana yace
"Buh dude i think she's ok the way she's every thing is
well backege"
Dariya sosai suka sa hadda tafawa da Wale wanda hakan
se daya sa Christoph murmusawa
Daniel yadan dafa kafadar Christoph yana fadin
"Wai kasanta ne?"
Girgiza kai yayi ya cigaba da danna wayar sa Daniel yadan
yi shiru kamar yana son cewa wani abu daga baya kuma
ya yi shiru kawai.
Tashi Mercy yayi yana gyara rigar shi wacca take armless
duk muscles dinta sun fito yana binsu da kallo hade da
nunu wrist watch din dake maqale a hannun nasa Rolex
yace
"Guys we're wasting time by 6:00 we should be at that
place and now it almost 5:40 we're running out of time"
Nan da nan suka miqe kowa ya dauki abun sa me amfani
kana Wale ya kalli Christoph da bashi da niyyar tashi yace
"Chriss are u not coming?"
Girgiza kai yayi yana fadin
"No i'm not coming we meet tomorrow"
Tashi yayi har inda car dinsu tayi parking ya raka su har
sun shiga motar su gate man ya bude Dan ya leqo ta
window motar ya dan daga murya yana fadin
"Jay about that babe Angelina"
Dariya Christoph yayi yana fadin
"We talk about that shit tomorrow"
Daria suka yi yana daga musu hannu har motar su ta
fice,kallon su Zulfa'u tayi tana mamakin su dan duk cikin
su ba me shigar kirki kamar wasu mata daga me sarqa se
me dankunne.
Komawa yayi ya zauna ya cigaba da abinda yake yi,wani
dan yaro ne ya fito daga flat din wanda bazai wuce su
Fudel a shekaru ba yana fadin
"Uncle Jay! Uncle Jay!"
Ya fada kansa,daga shi yayi yana juya shi hade da fadin
"Yesss my boi"
Shi kuma se bingira dariya yake ya saba shi a kafada suka
shige site din.
Har Salim ya tafi tunanin su Christoph bai bar brain dinta
ba.
No comments:
Post a Comment