Kaddara ta chapter 3

KADDARA TA Chapter 3

Tunda ta dawo tayi shigewar ta daki koda Anti farida ta
duba dakin gani tayi tana bacci,murmushi tayi sannan ta
isa bakin gadon tana taba qafar ta,da kyar ta miqe zaune
tana mitsitstika ido
"Bacci haka kamar wata kasa"
Mika take yi cike da shagwaba tana fadin
"Oh Anti farida "
Dariya take tana fadin
"Wake up wake up,tashi kiyi wanka kici abinci tun dazu fa
kike bacci ga can babies dinki sun dame ni ina mum take"
"Anti farida bar ni nayi bacci yau da ciwon kai na tashi tun
safe"
"A'ah bacci ya qare se na dare kuma"
Badan taso ba haka ta tashi ta shiga toilet tayi wanka
bayan ta fito ta saka dugowar riga ta dawo down stairs.
Suna gama cin abinci Fausam da Fudel suka zagayeta se
da ta musu assignment dinsu.
Da dare after isha'i tana daki ta kira maman su tana
picking suka gaisa se shagwaba take zuba mata
"Mama nidai gaskia wannan hutun kano zan dawo"
Girgiza kanta ta fara kamar a gaban Zulfa'u maman nata
tana fadin
"A'ah Zulfa'u kar ma ki fara,kiyi zaman ki anan
concentrate on ur studies,ki fito da result me kyau
wannan karon ma.kinji koh?"
Badan taso ba tace toh,suka yi sallama ta kira Salim,yana
dauka yace
"Hello babe"
Kwanciya sosai tayi akan gadon kana ta turo baki kamar
yana gaban ta tace
"Hi"
'yar dariya yayi yana fadin
"Yau 'yar shariya ce ba'a son yi min magana,bayan ni ne
yakamata nayi fushi kwana da kwanaki an manta ni"
Shiru tayi masa shi kuma ya cigaba da fadin
"Ok toh i'm sorry sweetheart bazan qara ba"
Murmushi ne ya subuce mata wanda se daya ji hakan
yasa shima dadi ya kama shi yana fadin
"Yawwa sweetheart dafantan dai an daina fushin dani?"
"Eh"
Girgiza kai yayi kaman yana gaban ta sannan suka shiga
tadi kamar basu ne suka gama fada yanzu ba.
Salim saurayin Zulfa'u ne wanda tun suna secondary yake
sonta har ma a gida an san da maganar su auren me dai
har yanzu ba'a yi ba suma anan Abuja suke da zama.
A cikin week din nan suka fara exams dan ta ajiye komai
a gefe karatu kawai take dan Zulfa'u badaga nan ba wajen
karatu.
Suna tsaka da exams Ummi ta kira ta tana zaune a daki
tana duba wasu books wayar ta tayi qara,dauka tayi tana
fadin
"Hello Ummi"
Shiru tayi tana jin ta daga baya tace
"Okay se kin shigo"
Tana nan zaune taji sallamar Ummi se dai bata kawo suna
tare da su Mary ba,da sauri ta sauko daga stairs din tana
ji suna gaisawa da Anti farida gabaki dayan mood dinta ya
canja hakan nan dai ta sakko ta same su itama ta zauna
kusa da Ummi suka fara gaisawa."Karatu fa yau nake so ki koya mana dan kinsan ba iyawa
nayi sosai ba"
Ta dan tsuke baki Zulfa'u tana fadin
"Me fa?"
Zaro ido Ummi tayi tana fadin
"Exam din da muke dashi gobe mana,pol science kema fa
kin san ban iya sosai ba"
"Su basu iya bane da baza su koya miki ba?"
Zulfa'u ta fada hankalinta kwance,sosai Ummi ke kallon ta
tana fadin
"Zulfa'u bana son rashin mutumci inkin san baza ki iya
koya mana ba se mu tashi muyi tafiyar mu"
Duk bidirin nan da suke yi a iya tsakanin su ne dan Anti
farida se tadi take dasu Mary.
Tabe baki tayi sannan ta tashi tace
"I'm coming"
Binta da kallo Ummi kawai tayi,ta dawo hannun ta da
books dinta sannan ta kalli Anti farida tana fadin
"Anti za muje compound muyi karatu"
Carpet me dan girma ta dauko musu hadda drinks da
snacks suka nufi compound din.
Kasancewar rana tayi sanyi se suka nemi gefen flowers
suka yi zaman su.
Gabadaya a takure Zulfa'u take sam bata son hulda da su
amma badan taso ba tana cin magani tana komai haka ta
koya musu.
Bayan sun danyi karatun na tsawan 1hr suka dan fara tadi
wanda Zulfa'u kam bata saka musu baki se dai tayi yake
ko kuma tace eh ko a'ah
"Gaskia ur Anti is nice,tana da kirki sosai i like her gata
me kyau,she's beautiful kamar babies dinta"
Inji Ada,dan murmushi tayi Zulfa'u kana ta maida hankalin
ta kan wayar ta da take dannawa.
Bude gate din da aka yi ne yasa su maida kallon su kan
katuwar motar data shigo land cruiser kalar dark brown
kamar sabuwa,sosai suke bin motar da kallo wanda
Zulfa'u kam hankalin ta yana kan wayar ta da take
dannawa dan ta bawa gate baya.
"Zulfa'u yaushe kuka yi new neighbours?a iya sani na
maman jafar sun tashi tunda jimawa"
Inji Ummi ta fada still idon ta yana kan motar
"Basu jima da zuwa ba"
Ta bata amsa,bude kofar motar aka yi wanda lokaci daya
zaka ji yadda suke dariya da tadi da alama bama hausawa
bane jin yadda suke dariya kamar zasu fasawa Zulfa'u
kunne.
Juyuwa tayi hade da kai kallon ta kan motar wanda tun
shigowar su se yanzu ta samu gannin su ta cikin glasses
dinta.
Lokaci daya taji zuciyar ta ta buga wanda hakan ya zama
bakwan lamari a tattare da ita dan wadan da ta gani ba
karamin bugun zuciya taji ba.
Kana gannin su kaga riqaqqun cristains,su 5 ne wanda
duk kallon da kayiwa daya daga cikin su kasan akwai ji da
samar taka da kuma kudi,kamar wasu masu aykin qarfi
dan a murde suke dan ko ba'a fada ma kasan suna
ziyartar gym.
Daga me chain a wuya se me dan kunne da sarqa wanda
duk cikin se ba mai shigar kirki daga me wando iya
gwaiwa se riga wancca tasa thick muscles dinsu bayyana.Har suka shige dayan flat din Zulfa'u bata daina binsu da
kallo ba,tambayar kanta take dama neighbours din nasu
Christians ne?
"Wow the look Aderobale"
Muryar Mary ce ta dawo da ita daga tunanin data
fada,lokaci daya kuma ranta ya qara baci dan jin abinda
Mary ta fada
"Amma neighbours din nan naku suna da kyau they look
handsome bayan hakan ma suna da kudi"
Ji tayi kamar ta kife Mary da mari lokaci daya ta hau
tattara books din tana fadin
"I think i will be going inside"
Suma tashi suka yi Ummi tana fadin
"Muma wucewa za muyi"
Se da suka gama maida kayan suka yiwa Anti farida
sallama sannan ta rako su bakin gate,Ada tace
"Thank u"
Dan murmushi tayi tana gyara zaman eye glasses din nata
suka wuce Ummi tana daga mata hannu tace
"Bye see u tomorrow"
"See ya! "
Se data ga wucewar su sannan ta koma ciki amma idon ta
yana kan motar da tayi parking.
A parlour ta samu Antu farida ta fada kan kujera tana
fadin
"Washh !"
Dariya Anti farida ke mata tana fadin
"Lazy kawai se kace wanda tayi wani aiki"
Murmushi kawai tayi tana shafa kan Fausam dan har
yanzu tunanin neighbours din nasu bai bar brain dinta ba.
Bayan sunyi dinner a parlour suna zaune kafin ta wuce
daki ta kalli Anti farida tana fadin
"Anti dama neighbours din mu ba musulmai bane?"
Dan girgiza kai tayi tana fadin
"Ba Christians bane musulmai ne dan sunan matar gidan
Maryam itama tama da en yara su biyu mace da namiji
kamar fudel da fausam"
Sosai Zulfa'u take binta da kallo tana mamakin kuma
wadan da suka zo dazu watakila baki ne
"Me kika gani?"
Da sauri ta girgiza kai cikin zuciyar ta tana fadin toh ma
ina ruwa na dasu?
"Kema fa yakamata kije ku gaisa da ita dan tana da kirki
sosai"
"Insha Alllah zanje"
"Yaushe ne gama exams din naku?se next week koh?"
Cike da tsoro Zulfa'u ta kalli Anti farida lokaci daya suka
sa dariya tana fadin
"Ki rufa mana asiri Anti ai se abun ya mana yawa,gobe
insha Allahu za mu gama"
Dariya tayi tana fadin Allah ya sa aga result me kyau,10:40
nayi ta wuce daki ta fara shirin bacci.
Tana tsaye a gaban mirror taji hayaniya a compound din
nasu,kasancewar ta window nata ana kallon tsakiyar
compound din yasa ta leka.
Wadan nan din dai ta hango sun zo bakin motar suna
magana wanda har Zulfa'u dake binsu da kallo tana dan
jiyu wasu abubuwan,kana jin yadda suke magana kasan ba
hausawa bane.
Su 4 ta gani sun shiga motar,shi kuma yana tsaye a wajen
har motar su ta fice.
Sosai Zulfa'u take son kallon fuskar sa amma bata ganshi
ba dan babu haske sosai a tsakiyar compound din,tana
gannin sa har ya koma ciki.
Tsaki taja kana ta kashe wuta hade da kwanciyar ta,5mins
yayi yawa bacci ya dauke ta.
Kamar daga sama ta fara jin kida wanda yasa ta tashi
zaune tana duba agogon dake side rower nan da nan ta
hau jan tsaki dan karfe 11:58 ya nuna mata
Eye glasses dinta dake ajiye kan side drower ta saka hade
da tashi ta leka window ta hango window ndake kallon
nata taga wutar a kunne amma gabadaya wutar site din
ma a kashe take.
Hakan nan yau ma tayi bacci rabi da rabi.

No comments:

Post a Comment