KADDARA TA Chapter 2
Yau ma kamar kullum tana sauka a school ta wuce class
dinsu wanda baya rabo da hayaniya da surutai,hankalin ta
kwance ta samu seat ta zauna bata kula kowa ba dan ita
bata fiye shiga shirgin kowa ba a cewar ta itama tata
matsalar ta ishe ta.
Tunda ta dago suka hada ido da Ummi da Mary dake nufu
ta ta hade rai kamar ba ita ce ta shigo yanzu da fuska a
sake ba.
Suna isowa inda take Mary tace da hausar ta bata fita
daidai
"Zufla'u har kin iso?tun dazo muku jiran ki a front door"
Badan taso ba ta danne zuciyar ta ta dago tana kallon su
Mary tace
"Yanzu nima na iso"
Ada dake zaune kan seat din dake kusa dana Zulfa'u tace
"Hope all is well?"
Dan kawar da kai tayi tana fadin
"Yeah"
Tunda ta amsa su ta maida hankalinta kan book din da
take karantawa se dai can qasan zuciyar ta ji take kamar
ta shaqe Ummi dan ita ta gayyato su Mary.
Ana gama lectures din yau taja hannun Ummi zuwa toilet
ran nan nata a bace tunkan su isa Ummi ke fadin
"Zulfa'u ina za muje haka?let off me kar kisa na fadi
mana"
Cike da masifa ta juyu tana fadin
"Ummi don't push me to do wall kisaka nayi abinda bai
kamata ba,ki daina gayyato mun arnayen qawayen ki inda
nake kin san bana son hulda dasu inda karatu ne yaci ace
zuwa yanzu kin haddace,ki daina kawo mun su inda nake
idan ba haka ba duk abinda na muku ke da su ku kuka ja"
Tsaki Ummi tayi tana fadin
"Wai Zulfa'u mesa kike abu kamar wata jahila ne?"
Cike da masifa a fusace tace
"Jahilar ce se me?call me whatever u want amma bazan
gaji da gaya miki ki daina kawo mun su inda nake ba"
Dafe kanta Ummi tayi sannan ta sassauto murya tana
fadin
"Haba Zulfa'u,wani lokaci idan kina wasu abubuwan kamar
ba me hankali ba,Christians dina nan da musulmi duk
Allah ne ya halicce mu kuma bai ce mu qamace su
ba,bayan haka banga abinda suka miki ba amma kin dora
karan tsana akan Christians din nan ba dama su rabe ki
kin dunga wasu irin abubuwa kamar me iskanu haba
Zulfa'u"
Tsaki taja tana fadin
"Ni dai na fada miki indai zaki zo inda nake ki daina
gayyato mun arnayen qawayen ki,tunda baki da wadan da
za kiyi hulda dasu se arna"
Tana kaiwa nan ta wuce fuu kamar iska tayi gida Ummi ta
bita da kallo.
A qufule ta shigo gidan tunda Farida ta kalle ta tasan an
mata wani abun amma ta share kawai dan tasan halin
qanwar tata.
Farida ita ce ta farko a wajen Baban su Alhj.Khalid da
mamar su Haj.Rakiya.
Baban su dan kasuwa ne dake zaune a garin kano wanda
Allah ya bashi rufin asiri daidai gwargado dan bai ragi
iyalinsa da komai ba.
Matan sa biyu Rakiya ita ce ta farko yaranta 4 farida ce ta
farko se Aliu,mariya da kuma Zulfa'u wato last born dinsu
dake zaune wajen yayar tasu a Abuja tana makaranta a
Nile university tana karanta business admin,dan duk wata
dawainiya farida ce ke mata dan ta dawo wajen ta tun
lokacin da tayi aure.
Se matar sa ta biyu wato Karima da yaranta duk maza
Abubakar da Jabir.
Duk yaran gidan mata sunyi aure tun suna gama secondry
amma Zulfa'u ce kawai tayi sa'a baban nasu ya bar ta
qarasa har uni dan yanzu haka ma level 200 zata shiga.
Sa'ar ta daya baban ta yana da mungun sauqin kai banda
mamar su da take me zafi dan abu kadan zaka mata
tahau fada se dai itama wasu lokutan akwai sauqin kai.
Tana da wata dabi'a na rashin son wanda ba musulmi ba
dan ko yaya ka rabe ta se ta nuna maka,se dai tana da
sauqin kai wasu lokutan amma abu kadan ne ke sata fushi
a wani lokacin.
Haka ma yayan ta Aliu dan shima kusan halin su daya
basa son hulda da wanda ba musulmi ba har abun nasu
ya so yayi yawa.
Yadda Zaka sayi data mai matukar sauki a layin Ka na MTN, yadda zaka sayi data 200Mb akan #50
Yadda Zaka sayi data 200Mb akan #50 a layin Ka na MTN
Kamar yadda kuka gani a Wanan hoton zaka dial na Wanan code din *121*1# Sai kayi select na datar dakaga zasu baka
Allah taimaka

KADDARA TA chapter 1
KADDARA TA Chapter 1
Hayaniya sosai ake cikin class din dauke da mutane,duk
da ba wani yawa ne dasu ba amma hakan bazai hana ka
jin yadda hayaniyar tasu ke tashi ba.
Duk wannan hayagagar bata hana Zulfa'u duba book din
dake gabanta ba hasalima tamkar bata san ana yi ba dan
karatun ta take hankali kwance.
Wasu emmata ne da baza su wuce age mates din ta ba
suka zauna kusa da ita.
Dafa kafadar ta da Ummi tayi ne ya bata damar dagowa
tana gyara zaman glasses din dake makale a fuskar tata.
"Babe karatun ne?"
Hada idon da suka yi da dayar ne yasa ta hade rai ta
tsuke baki badan ta so ba ta daga mata kai alamar
eh,gannin haka ne yasa Ummi juyuwa ta kalli wacca ke
gefen nata me suna Mary tace
"Mary you should just wait for me at the front door I will
catch up with you there"
Murmushi tayi mata hade da miqewa ta bar wajen.
Ummi ta maida kallon ta kan Zulfa'u data maida hankali
kan book din nata tace
"Haba Zulfa,wai mesa kike haka ne?is she not a human
being like you? ki daina irin haka ba kyau"
Ko kallon ta bata yi ba ta dan motsa bakin ta kamar bata
son yin magana tace
"As you can see I'm doing something important here,if
you can't shut your trap you are free to live"
tsaki Ummi taja hade da miqewa ta bar wajen wanda
haka yasa ta cigaba da karatun ta hankali kwance.
Suna gama lectures din ta fito daga class din riqe da hand
bag data rataya a kafada.
Duk da ba siririya bace amma bazaka kirata qatowa ba se
dai tana da dan jiki wanda ya bayyanar da yanayin qibar
tata.
Ba fara bace haka zalika ba baqa bace dan skin colour
dinta me tsada ce wacca ba kowa ke da irinta ba,tana da
eye balls masu girma da haske wanda suke qara mata
wani irin kyau na mussamman.
Tana da hanci daidai fuskar tata hade da dan madaidaicin
lips dinta masu kyau.
Masha Allah Zulfa'u kyakkyawa ce me dan madaidaicin
tsayi,shekarun ta 19 wanda hakan zai sa ka ga tsantsar
kyau da emmatan taka akan fuskar tata,se dai a koda
yaushe zaka hango farin medicated glass din dake duke
akan fuskar tata wanda shi ke taimakamata.
Duk da ba atampa ta saka ba wata riga ce kalar milk
wacca ta zauna daidai da jikin nata se dai ko kadan bata
matse ta ba hasalima se dai ace yawa suka mata,se dark
brown din wando data saka wanda shima bashi da
maraba da a kira shi da sun mata yawa se dai duk da
hakan kana gannin yanayin shigar ta kasan ta mutumci ce
kuma ta masu aji dan kayan masu tsada ne sannan ta
yafa farin mayafi bisa kanta dan ita tana son simple
rayuwa.
Direct gate ta nufa ta tsari abun hawa ta wuce gida.
Suna isowa bakin gate din ta bashi kudin sa hade da shiga
cikin gidan tana gaishe da gate man din shi kuma yana
mata sannu da zuwa.
Tsayawa tayi a bakin gate din tana qarewa filin gidan
kallo dan motoci ne reras aciki wanda sun kusan cika
katon filin gidan ga mutane suna ta zirga zirga a dayan
flat din kasancewar flat din biyu ne kuma duk up stairs.
Ta kai tsawan 3mins a haka tana qare musu kallo kana ta
tabe baki tayi wucewar ta dayan flat din.
Gida ne wanda ya amsa sunan sa gida dan ya hadu nesa
ba kusa ba,duk wani abun jin dadin rayuwa akwai shi an
zuba kamar baza a mutu a bar shi ba.
Sallamar da tayi ne yasa yaran dake zaune a parlour yin
kanta suna mata oyoyo.
Daga su tayi tana dariya wanda duk sun kanainaye ta tana
shirin faduwa qasa se dariya suke tsandarawa itama tana
taya su.
Da kyar ta samu suka sake ta ta shigo ciki ta zauna a
gajiye kan kujera.
Matar dake binsu da murmushi dake zaune kan kujera
kana gannin ta kasan matar gidan ce dan kamannin ta sak
da en yaran baza ta wuce 26 zuwa da 27 bah,fara ce
kyakkayawa tayi kyau cikin lace din da ta saka kalar pitch
"Sannu da gida Aunty Farida"
"Welcome,ya school din?"
"Alhmdulillah"
Ta fada tana relaxing sosai kan kujerar kana taja tsaki
tana fadin
"Wallahi Anti na gaji da school din nan"
Dariya sosai ta bata
"Kin gaji kuma,ay karatu yanzu aka fara tashi kije kiyi
changing ga can launch kici kizo ki huta,ku koma get up
mum ta dawo daga school ta gaji"
Ta qareshe maganar tana daga en yaran jikin ta ita kuma
tana murmushi gannin yadda Fausam ya shagwabe fuska
ta shafa sumar kansa tana fadin
"Yanzu zan dawo kar kayi kuka inba haka ba zamu bata"
Tuni ya wangale baki yana dariya ita kuma ta dauke jakar
ta har zata wuce daki ta juyu tana fadin
"Anti farida"
Ta dago tana kallon ta bata jira ta bata amsa ba tace
"Su waye suka zo?"
"Oh ne neighbours din mu ne suka dawo yau"
Yatsina fuska tayi tana fadin
"All those cars dana gani da mutanen a gidan zasu
zauna?"
Dariya Anti farida tayi tana fadin
"Who told you so?rakiya suka zo musu mana,gobe zan
shiga mu gaisa dasu"
Bata ce komai ba ta wuce saman daki abinta ta fada
toilet tayi wanka sannan ta yi shirya ta dawo suka ci
abinci.
Tunda ta dawo bata fita ba hasalima tana daki tana
karatu,da daddare around 11 taji neighbours din nasu sun
saka kida me uban qara,kamar tayi hauka dan ko kadan
bata son a dameta idan tana bacci.
Tashi tayi ta leka windowa kasancewar window dakin nata
yana kallon dayan site din wanda basu da tazara sosai.
Gabaki daya babu haske ma a site din da alama suma
sunyi barci se iya window dake kallon nata ne ta hango
wutar a kunne kuma da alama daga nan kidan ke tashi.
Tsaki taja ta koma gadon cike da bakin ciki tunkan aje
ko'ina neighbours din nasu sun fara shiga haqqinta.
Haka tayi baccin rabi da rabi washe gari da safe ta shirya
cikin doguwar riga abaya da bata kamata ba kamar koda
yaushe hasalima ta mata yawa ta yafa mayafin me dan
girma sannan ta dauki hand bag dinta ta sauko dinning
table.
Fausam da Fudel ne ke mata good morning ta zo tana
shafa kansu tana fadin
"Good morning my babies"
Sannan ta gaishe da Anti farida dake hada musu serving
abincin.
"How was your night?"
Jan kujera tayi ta zauna tana hatsina fuska hade da fadin
"It was terrible"
Dariya tayi tana fadin
"Yau kuma?"
"Ehh mana Anti,jiya baki ji neighbours dinki yadda suka
dame ni da kida ba kamar a club,sam basu san haqqin
makwaftaka ba"
Ajiye mata plate din chips tayi a gabanta da fried egg se
cup din black tea
"Ni banji komai ba"
Anti farida ta fada tana zama akan kujera,dan murmushi
Zulfa'u tayi tana fadin
"Anti yadda kike da nauyin baccin nan ina zaki ji kowa"
Haka nan dai suna tadi har suka gama break fast din har
compound din nasu Farida ta raqo su dan driver ne ke
kaisu ita da su Fausam dan suma sun shirya.
A compound din nasu ta ga babu sauran cars din da
alama sun jima da tafiya se wasu guda 5 haddadu da aka
yi parking dinsu a parking lot.
Tabe baki tayi ta shige motar suna dawa Anti farida hannu
gate man ya bude musu gate suka fice ita kuma ta koma
ciki.

Barka da zuwa
Assalamu'laikum
Muna muku barka da zuwa wanan shafi namu Mai albarka muna rokon Allah alkairai garemu gaba daya
Allah yasa wanan shafi ya kasance Mai amfani ga al'ummah Ameen

Subscribe to:
Comments (Atom)